Rashin Tsaro:An ci gaba da ruguza maboyar masu aikata miyagun laifuka a hanyoyin dogo da ke Gwarimpa.

0
60

An kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi guda biyu da  wasu uku da ake zargi da aikata laifuka

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta sha alwashin ci gaba da ruguza gine-gine da kasuwanni da gidajen kwana da aka gina a kan titin jirgin kasa da ke Gwarimpa.

Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello da kwamishinan ‘yan sanda, Sunday Babaji, sun sake jaddada kudirinsu na kawar da duk maboyar masu aikata laifuka a babban birnin kasar nan.

Da yake jawabi a madadin gwamnatin, babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tabbatar da tsaro ga ministan babban birnin tarayya, Kwamared Ikharo Attah ya bayyana haka nan take bayan aikin tsaftace muhalli a Gwarimpa.

Tawagar ayyukan hadin gwiwa wacce ta kunshi manyan jami’an FCTA, Sojojin Najeriya, Rundunar ‘yan sandan Najeriya, Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Jami’an Tsaro da Civil Defence, Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NDLEA), Hukumar Kula da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Ma’aikatar Jiha.
, Directorate of Road Traffic Services, da kuma Abuja Environmental Protection Board (AEPB) sun mamaye titin jirgin kasa ba tare da sanar da fara rusa rumfuna , kasuwa da kuma yan bata.gari.

Attah ya ce: “Abu na farko, korafe korafe yayi yawa,na  biyu, batun tsaftar gari matsala ce a nan,

“Kwamishanan ‘yan sanda, Sunday Babaji da DPO na ‘yan sanda a Gwarimpa sun samu rahoton aikata miyagun laifuka da ke faruwa a nan, mazauna yankin sun koka da yadda mutane ke kokarin boyewa a nan domin yin fashi a unguwanni kuma hakan ya kasance mai matukar tayar da hankali.

“A yau an kama wasu mutane dauke da miyagun kwayoyi, kuma hukumar NDLEA ta rundunar Command and Control JTF a karkashin CP na FCT da kuma DC Bernard Iwe ta kama.

“Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifuka, ita kuma hukumar NDLEA ta kama wasu mutane biyu masu safarar miyagun kwayoyi,, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da zuwa har sai sun bi doka da oda.

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa ba a fara amfani da filin ba, Attah ya ce, “Filin na Hukumar FCT ne kuma an tsara shi ne a matsayin hanyar wucewa ta hanyar Kubwa da ke waje da Arewa.

Kuma ‘yan sanda sun ba da shawarar cewa gwamnati ta gina shinge a kusa da shi. Don hana masu kutse”.

Da yake amsa tambayar manema labarai game da dorewar, ya ce, “A bara, mun share wannan wuri, kuma muna nan a yau, za mu ci gaba da zuwa har sai masu laifi da masu karya doka sun daina ko mu ci gaba da kama su .

“Gwarimpa zai kaimu sati daya, Kuje kuma ana cigaba da aiki,har da  Npape, titin filin jirgin sama wurin aiki ne akai akai kuma ko’ina a cikin birni ana kiran a tsaftace shi.

A halin da ake ciki, an ga ’yan kasuwa suna kwasar kayayyakinsu yayin da masu tuka babura ke yin sana’ar gaggauwa.

 

Daga Fatima Abubakar.