Rundunar sojin saman Nageriya NAF ta Nemi Afuwar kan wani Mummunan Harin Ba Za ta Da Aka Kai A Jihar Nassarawa

0
34

Rundunar sojin saman Nageriya NAF ta Nemi Afuwar kan wani Mummunan Harin Ba Za ta Da Aka Kai A Jihar Nassarawa

Rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta dauki alhakin wani harin bazata da ya afku a ranar 23 ga watan Junairun shekarar 2023, a yankin Rukubi dake karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa, wanda yayi sanadin asarar rayuka 37.

Shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana nadamar faruwar lamarin a wata ziyarar ta’aziyya da ya kai fadar Sarkin Lafia a ranar Juma’a

Abubakar, yayin da yake jawabi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ya bayyana cewa harin da aka kai ta sama ba bisa ka’ida ba ne, inda ya bayyana cewa NAF ta gudanar da aikin ne a matsayin mayar da martani ga ayyukan miyagun laifuka da hare-haren ta’addanci da suka hada da sace daliban firamare a yankin.

Dangane da bayanan sirri da ke nuni da kasancewar ‘yan ta’adda a kan babura, an kai harin ta sama, wanda ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya amince da koke-koke da damuwar jama’a game da lamarin, wanda ya sa NAF ta gudanar da cikakken bincike.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa, hakika harin na sama ya shafi fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba

A duk lokacin da ake zargin sojoji da kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, yana da zafi a gare mu,” in ji shi.

Ya kara da cewa ziyarar jihar Nasarawa an yi niyya ne domin jajantawa gwamnati da iyalan da abin ya shafa, wanda hakan ya kawo karshen afkuwar hatsarin.

A yayin ziyarar, Air Marshal Abubakar ya bayar da tabbacin yin gaskiya da rikon amana a dukkan ayyukan sojojin, inda ya bayyana matakan da suka dauka na hana sake afkuwar irin haka a nan gaba.

Gwamna Abdullahi Sule ya yaba da shirin da rundunar sojojin saman Najeriya ta yi na jaje, inda ya bayyana hakan a matsayin wani sabon salo da zai taimaka wajen kawo karshen lamarin.

Gwamnan ya kuma yabawa rundunar sojin saman Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a jihar, inda ya yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafi ga ayyukansu.

A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Bage Muhammad (mai ritaya), ya bayyana godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya da Shugaban Rundunar Sojan Sama bisa jajewar da suka yi musu, inda ya yi nuni da muhimmancin neman afuwar wajen samun waraka.

Ya ce: “Wannan sabon abu ne; cewa hukuma kamar rundunar sojin saman Najeriya, da ta gudanar da aikin da aka ba su izini amma wani hatsari ya faru a bakin aiki, su karba su dawo su ba su hakuri, abu ne da bai taba faruwa ba a baya.”

 

 

Hafsat Ibrahim