Rundunar Yan Sanda A Jihar Gombe Za Ta Buɗe Sabon Ofis A Wuro Biriji

0
19

Rundunar Yan Sanda A Jihar Gombe Za Ta Buɗe Sabon Ofis A Wuro Biriji

Daga Yunusa Isa, Gombe

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe CP Hayatu Usman, ya yi alƙawarin samar da ofishin ƴan sanda a Anguwar Wuro Biriji, don ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a yankin Bypass Dake cikin garin Gombe.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a zauren Digacin Wuro Biriji, yayin da ya ziyarci anguwar don ƙarfafa alaƙa tsakanin ƴan sanda da al’ummar yankin.

Da yake jaddada cewa yankin na Bypass yanki ne mai ɗimbin jama’a, Kwamishinan yace da zarar an samar da ofishin da ya dace, rundunar ‘yan sandan jihar za ta tura jami’ai da dakarunta zuwa yankin don samar da ingantaccen tsaro.

Ya kuma yi ƙira ga al’ummar yankin su marawa rundunar baya ta hanyar ba ta muhimman bayanai dama kai rahoton duk wani abin da basu gamsu da shi ba.

Da suke jawabi a madadin al’ummar anguwar, Shugaban Kungiyar Ci Gaban Wuro Biriji Dr Sulaiman Garba da wani dattijon anguwar Malam Sulaiman Muhammad, sun koka kan ƙaruwar aikata miyagun laifuka a yankin, suna masu ƙira ga rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta samar musu da caji ofis don kai ɗauki cikin gaggawa da samar da dauwamammen sintiri a lungu da saƙo.

Sun kuma yi alƙawarin bai wa ‘yan sanda cikakken haɗin kai da goyon baya don samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar ’yan banga ta Danga Security Patrol a anguwar, Alhaji Idris Sa’ad, ya bada tabbacin cewa nan ba da jimawa ba al’ummar anguwar za su samar da ofishin da ya dace ya caji ofis.

Ya jaddada ƙudurinsu na haɗa kai da ‘yan sanda, wajen kakkaɓe miyagun laifuka a anguwar tare da tabbatar da tsaro.

A jawabinsa na godiya, Digacin Wuro Biriji Alhaji Sani Adamu, ya yabawa kwamishinan ‘yan sandan bisa ziyarar, yana mai cewa buɗe ofishin ‘yan sanda a anguwar zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafa tsaro a yankin Bypass baki ɗaya.