Kwamandan Civil Defence A Gombe Ya Karɓi Baƙuncin Al’ummar Bojuɗe, Ya Nemi Haɗin Kai, Tare Da Ba Su Tabbacin Samun Karin Caji Ofis

0
12

Kwamandan Civil Defence A Gombe Ya Karɓi Baƙuncin Al’ummar Bojuɗe, Ya Nemi Haɗin Kai, Tare Da Ba Su Tabbacin Samun Karin Caji Ofis

Daga Yunusa Isa, Gombe

Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Jihar Gombe (NSCDC) ya karɓi baƙuncin shugabannin al’ummar Bojuɗe a wata ziyarar ban girma da yabo bisa ayyukan rundunar a yankin.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Hakimin Bojuɗe Injiniya Muhammad Ibrahim, yace sakamako kafa caji ofis ɗin hukumar ta Civil Defence tare da daga darajarsa zuwa baban ofishin yanki, al’ummar Bojuɗe da kewaye sun samu natsuwa har suna iya barci da ido biyu.

Yace kasancewar jami’an hukumar ta Civil Defence ya inganta sha’anin tsaro a yankin, musamman wajen dakile rikicin manoma da makiyaya.

Hakimin yace al’ummar yankin sun samar da ƙarin fili don buɗe ƙarin caji ofis na rundunar musamman a kan iyakokin garin na Bojuɗe da ƙananan hukumomin Nafaɗa, Funakaye, Dukku da kuma Akko.

Ya yabawa hukumar ta Civil Defence da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da sauran jami’an tsaro a jihar bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Bojuɗe dama Jihar Gombe baki ɗaya.

Tun farko a nasu jawaban, wasu dattawan garin Alhaji Ahmed Bojuɗe, da Babayo Abdullahi, da Alhaji Ado Gabani da kuma Muhammad Musa Kolo, sun yabawa kwamandan hukumar na jiha bisa yin ruwa da tsaki wajen buɗe caji ofishin din rundunar a Bojuɗe, suna masu bayyana hakan a matsayin wani babban matakin da ya inganta zaman lafiya da tsaro a yankin.

Sun kuma yi ƙira ga gwamnatin jihar ta ƙara baiwa rundunar tallafi musamman ta hanyar samar mata da motocin sintiri da kayan aiki da kuma makamai.

Da yake nashi jawabin, kwamandan hukumar ta Civil Defence a Jihar Gombe Muhammad Bello Mu’azu, ya baiwa al’ummar Bojuɗe tabbacin samar musu ƙarin caji ofis, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Sai dai ya bukaci al’ummar yankin su taimaka wajen samar da ofis da matsugunin da suka dace, yana mai ba da tabbacin cewa “Da zarar kun samar mana da ofis da wurin kwana da suka dace, na ba ku tabbacin zan tura muku dakaru da ma’aikata”.

Da yake neman ƙarin haɗin kai da goyon baya daga al’ummar yankin ga hukumomin tsaro, kwamandan ya buƙaci mutanen na Bojuɗe su kai rahoton duk wani take-taken da basu gamsu da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa don ɗaukar matakin gaggawa.

Bello Mu’azu ya gargaɗi al’ummar yankin su guji boye masu laifi da masu tsegumta musu bayanai, yana mai cewa masu tsegumta bayanan sun ma fi masu aikata laifukan hatsari.

Ya kuma shawarci shugabannin gargajiya na yankin su lalubo hanyoyin tantance baƙi da sabbin mazauna anguwanninsu, tare da miƙa wa hukumomin tsaro bayanansu.

Kwamandan yace matakin zai taimaka wajen magance ta’addancin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda yace suna ƙoƙarin mamaye yankuna kamar Jihar Gombe.

Da yake yabawa da irin haɗin kai da fahimtar juna da ake samu tsakanin al’ummah da hukumomin tsaro a jihar, Kwamandan na Civil Defence ya yabawa gwamnan Jihar Muhammadu Inuwa Yahaya bisa jajircewarsa na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin al’ummar jihar.

Ya ƙara da cewa jajircewar gwamnan na baya-bayan nan wajen magance rikice-rikicen manoma da makiyaya ta hanyar haɗa kai da jami’an tsaro ya samu gagarumar nasara ta fiye da kaso 85 cikin ɗari.

Yace idan aka ci gaba da hakan, babu shakka za a samu ƙarin nasarori.