Shugaba Muhammadu Buhari ya isa faretin sojoji a jiya Alhamis cikin kayan soji.

0
78

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa bikin kaddamar da bikin taron sojojin Najeriya na 2023.

Buhari wanda ya isa dandalin Eagle Square, inda aka yi faretin, da misalin karfe 10:18 na safe ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.

Janar din sojan mai ritaya yana sanye ne da kakin soji na bikin, kuma a halin da ake ciki shugaban ya duba sama da hafsoshi 1,000 da ke shirin faretin.

An  ruwaito cewa babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor; babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Gen. Faruk Yahaya, da Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Baba su. ma  sun halarci taron.

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

 

Daga Fatima Abubakar.