Ana kyautata zaton cewa akwai ‘yan Najeriya da yawa cikin wayanda suka mutu a wani coci da ke Kenya.

0
15

Ana fargaban cewa wayanda suka mutu a coci a Kenya akwai yiwuwar akwai ‘yan Najeriya.Kuma  kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na wadanda abin ya shafa yara ne, wadanda aka gano gawarwakinsu a nannade da auduga a cikin ramukan da ba su da zurfi.

Shugaban Kenya William Ruto ya lashi takobin daukar mataki kan fastoci masu da’a irin su Nthenge “wadanda ke son amfani da addini wajen ciyar da munanan akidar da ba za a amince da shi ba”.

An kama Nthenge wanda aka san shi da koyarwar tsattsauran ra’ayi a baya.

An kama mai wa’azin telebijin ne a shekarar 2017 kan zargin “tsatsa jiki” bayan ya bukaci iyalai da kada su tura ‘ya’yansu makaranta, yana mai cewa Littafi Mai Tsarki bai gane ilimi ba.

An sake kama Nthenge a watan da ya gabata, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana, bayan da wasu yara biyu suka mutu da yunwa a hannun iyayensu.

An bayar da belinsa kan kudi shilling 100,000 na Kenya kwatankwacin dalar Amurka 700 kafin ya mika kansa ga ‘yan sanda bayan harin da Shakahola ya kai.

A ranar 2 ga watan Mayu ne Nthenge zai gurfana a gaban kotu.

 

Daga Fatima Abubakar.