Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta tabbatar da sake buɗe rukunin shagunan kasuwanci na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja bayan rufe su da aka yi sakamakon wata tashin-tashina, da ya faru a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2024.
Lamarin rufewar ya faru ne a Ranar Lahadi 19 ga watan nan rundunar sojin ta rufe wajen, domin gudanar da bincike kan ayyukan da ta bayyana a matsayin masu aikata ɓarna. Musamman ga Jami an to sai dai kafin rufewar an ga wani bidiyo na yawo a shafukan intanet inda wasu mutane suka far wa wasu sojoji a kusa da rukunin shagunan…
Bidiyon ya nuna yadda wasu jami’an ƴansanda suka shiga tsakani domin ceton jami’an sojin da mutane suka riƙa kai wa duka da jifa.
Da yake sanar da sake buɗewar a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Darektan hulɗa da jama’a na rundunar sojin Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce matakin sake buɗewar na daga cikin matsayar da aka cimma a taron da aka yi a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, da shugabannin rukunin shagunan da sauran shugabannin hukumomin tsaro na Abuja.
Janar Onyema, ya ce daga cikin matakan da aka ɗauka a taron har da rufe shago mai lamba C93, da kuma kama masu shagon da aka yi rikicin.
Hafsat Ibrahim