Tsaikon da ya haddasa rashin gurfanar da Sirika a gaban kotu, yau Talata.

0
11

Shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika da wani ɗan uwansa, Ahmad Sirika, a yau talata a wata sabuwar shari’ar kan badakalar kwangilar da ta kai naira biliyan 19.4 ya samu tsaiko sakamakon rashin kasancewarsu a gaban alƙali.

Gidan talbijin na Tozali TV ya rawaito: lauyan Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa alkalin kotun, Mai shari’a Suleiman Belgore, cewa ba a sanar da tsohon ministan da dan uwansa abin da ake tuhumar su ba, a shari’ar.

Don haka lauyan ya buƙaci a ɗage shari’ar, buƙatar da alkalin ya amince da ita.

Daga baya alƙalin ya sanya ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gurfanar da su gaban kotu.Hukumar EFCC na tuhumar tsohon Ministan ne da ɗan uwansa a wannan karon, da abubuwa takwas da suka jiɓanci tsabar kuɗi har naira biliyan 19.4.

Adadin dai an ce na wasu kwangilolin ma’aikatar sufurin jiragen sama ne daga tsohon ministan zuwa kamfanin Enginos Nigeria Limited wanda ake zargi mallakar ƙanin nasa ne.

A makon da ya gabata ne aka gurfanar da Sirika da diyarsa Fatima da kuma sirikinsa a gaban kotu kan zargin badaƙalar naira biliyan 2.7, inda daga bisani kotu ta bayar da belinsu.

 

 

 

Hafsat Ibrahim