Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Yakubu Dogara, ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa ga sauye-sauyen da ya yi a harkar zabe a Najeriya, musamman ganin yadda aka bullo da tsarin tabbatar da ingancin zabe (BVAS) a harkar zabe.
Dogara ya ce Buhari na iya yin sunansa da zinare a matsayin gwarzon dimokuradiyyar Najeriya idan ya bibiyi yadda aka yi gyaran fuska a zaben kasar nan a 2023.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Turaki Hassan, Dogara, wanda kuma shi ne shugaban jami’ar Achievers’ da ke Owo ta Jihar Ondo ya raba wa manema labarai a wajen taro karo na 12 na cibiyar. Ya ce kalubale ne ga daukacin ‘yan Najeriya wajen ganin an aiwatar da sauye-sauyen a zaben 2023 mai zuwa.
Dogara ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su siyar da kuri’unsu ko kuma su ki kada kuri’a. Yana mai cewa, “Ku tuna cewa mulki yana cikin kuri’ar ku, kuri’ar ku ita ce makomarku. Don haka, kar ku sayar da shi kuma kada ku ajiye shi a cikin dakin ku, dole ne ku yi amfani da shi. Ku shiga ta hanyar fitowa da yawa don jefa kuri’a don lamirinku.”
Ga daliban da suka yaye, ya ce, “Kuna da burin ku kuma na tabbata burinku a bayyane yake. Ina yi muku wasiyya da ku kasance masu hazaka ba tare da tsoro ba. Yanayin yana da wahala sosai amma ku jajirce. Aikin Jami’ar Achievers misali ne mai kyau wanda har yanzu za ku iya cimma burinku tare da zama abinda kuke so da yardar Allah.
Ina shawartar ku da ku shiga cikin wannan alherin ta hanyar himma a cikin duk abin da kuke yi kuma ku ci gaba da bin manufofinku tare da girman mutunci da tsoron Allah.
Daga Fatima Abubakar.