Tsohon shugaban kasa ya rasu

0
73

 

Tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf ya rasu a wani asibiti da ke birnin Dubai bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda wasu majiyoyin soji suka tabbatar wa Al Jazeera a jiya Lahadi.  Ya kasance  yana da shekaru 79.

Musharraf, Janar mai tauraro hudu, ya mulki Pakistan kusan shekaru goma bayan ya kwace mulki a wani juyin mulkin da babu zub da jini  a shekarar 1999.

Tsohon janar din yana fama da amyloidosis – cuta mai lallata gabobin jiki.  Ya dade yana kwance da keken guragu.

A cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa da bangaren yada labarai na rundunar ya fitar, manyan hafsoshin sojin sun bayyana “ta’aziyarsu” kan rasuwar tsohon shugaban kasar.

 

“Allah ya jikan wanda ya rasu, ya kuma baiwa iyalansa hakuri da juriyan rashinsa.”

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho