Gwamna Badaru ya nada Sunusi a matsayin sabon Sarkin Dutse

0
9

Gwamna  Muhammad Badaru na Jigawa ya amince da nadin Hameem Sunusi a matsayin sabon Sarkin Dutse.

 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa sabon sarkin ya gaji mahaifinsa, Dr Muhammad Sunusi II wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Janairu yana da shekaru 79, bayan ya shafe shekaru 28 akan karagar mulki.

 

NAN ta kuma ruwaito cewa sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abdulkadir Fanini ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a Dutse ranar Lahadi a madadin gwamnan jihar.

 

Gwamnan ya ce an zabi sabon sarkin ne bayan an yi nazari sosai kan sunayen da sarakunan masarautar Dutse suka ba da shawarar.

 

Ya kuma bukaci sabon sarkin da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na al’ummarsa, ba tare da fifita su ba, ya hada kawunan su domin ci gaban yankin.

 

NAN ta ruwaito cewa har zuwa lokacin nadin sabon sarkin, wanda aka haifa a shekarar 1979, ya rike mukamin Dan’iyan Dutse.

 

“A madadin Gwamnatin Jihar Jigawa, Mai Girma Gwamna Muhammad Badaru Abubukar ya taya Mai martaba Alhaji Hameem Nuhu Sanusi murna bisa nadin da aka yi masa tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya da kwanciyar hankali a matsayin Sarkin Dutse,” inji shi.

 

Da yake mayar da martani, sabon sarkin wanda ya nuna jin dadinsa ga gwamnan da ya zabe shi a matsayin wadda ya cancanci wannan mukamin, ya yi alkawarin tabbatar da amincewar da aka yi masa.

 

Sunusi, wanda ya yi alkawarin aiwatar da manufar bude kofa, ya bukaci goyon baya da hadin kan kowa da kowa a masarautar.  (NAN)

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho