Wasu matasa a jahar Bayelsa sun dauki mataki a hannun su yayin da wani matuki babur ya kashe fasinjan sa.

0
22

A ranar Laraba ne wasu ’yan daba suka kashe wani ma’aikacin babur a unguwar Kpansia da ke cikin babban birnin Yenagoa a jihar Bayelsa.

Wannan matakin ya biyo bayan zargin daba wa wani matashi wuka saboda rashin jituwa kan canjin naira hamsin.

An ce mahayin babur din ya daba wa matashin da ba a san ko wanene ba wuka  bayan sun yi jayayya kan canjin Naira 50. Wanda aka kashe din ya mutu nan take.

A fusace da matakin da ya dauka, wasu mazauna da ke kusa da wurin sun far wa mahayin Keke tare da kashe shi da duwatsu.

Ba a iya tantance sunayen mutanen da suka mutun ba har izuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da faruwar lamarin.

Rundunar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Asinim Butswat ya fitar, ta kuma yi Allah wadai da kisan da mahayin Keke ya yi wa matashin tare da kashe shi.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tura jami’an yaki da tarzoma domin dawo da zaman lafiya a Kpansia da kewaye, kan kisan gillar da wani matashin dan unguwarsu ya yi da wani direban babur.

“Matukin babur din ya daba wa matashin wuka har lahira saboda wata ‘yar rashin jituwa.

“Rundunar ‘yan sandan ta yi Allah-wadai da matakin da direban babur din ya yi, wanda kuma wasu fusatattun matasa suka kashe shi har lahira tare da yin kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu.

 

Daga Fatima Abubakar.