Zababben shugaban kasa ya yi ganawar sirri da Betara

0
42

A ranar Talata ne dan takarar shugaban kasa a majalisar wakilai ta 10, Muktar Betara, ya yi wata ganawar sirri da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

 

Betara, mamba mai wakiltar mazabar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar ta jihar Borno, ya na ta neman masu mara wa burinsa na zama kakakin majalisar wakilai baya a wajan mambobin jam’iyyar, zababbun ‘yan majalisar wakilai, tsofaffin ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki.

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na Campaign Betara ya bayar a Abuja Laraba.

“Yakin neman zabe da tuntubar Betara da zababben shugaban kasa na daya daga cikin tuntubar da ya fara yi cikin watanni uku da suka gabata gabanin rantsar da shi a watan Yuni.

 

“Betara wanda a halin yanzu yake shugabantar kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai, a baya ya yi musabaha tare da babban kwamandan mai jiran gado jim kadan bayan wani zaman daukar hoto.

“Ziyarar tuntubar Betera ga zababben shugaban kasa ta gudana ne a sabon gidansa da ke Defence House a Abuja, bayan dawowar shi daga hutu da kuma aikin ummura a Saudiyya,” in ji ofishin yakin neman zaben.(NAN)

 

Firdausi Musa Dantsoho