Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jaddada goyon bayan sa akan batun kafa ‘yan sandan Jihohi a Najeriya.
Gwamna Inuwa ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunibu ranar Talata a fadarsa dake Abuja, inda ya ce yunƙurin yana da matuƙar muhimmanci duk da lamarin sai ya bi ta majalisun dokokin ƙasa, kana ya sami sahalewar kaso biyu bisa uku na Majalisun dokokin Jihohi kafin zama doka.
A cewar Inuwa, “nayi imanin cewa ɗaukacin al’ummar Jihar Gombe suna da ra’ayin samar da ‘yan sandan jihohi, domin hakan zai sa tsaro ya daɗa matsawa kusa da jama’a ta yadda za mu iya sanya ido fiye da yadda wani zai sanya mana wajen kula da lamuran mu.
Haka kuma Gwamnan ya ƙara da cewa, duk da ance Gwamnoni sune jagororin tsaro a jihohinsu, amma mutanen dake gaba-gaba a harkar ne ke kula da sha’anin tsaron wato manyan kwamandoji ko kuma kwamishinonin ‘yan sanda waɗanda ke karɓar umarni daga shugabanninsu na Abuja, toh kunga idan akwai ‘yan sandan jiha zamu iya sanya ido kan duk wani motsi tare da ɗaukar duk wani mataki cikin gaggawa”.
A hannu guda Gwamnan yayi wa Shugaban ƙasa ƙarin haske dangane da ci-gaban da ya samar a Jihar Gombe cikin shekaru biyar ɗin daya shafe akan karagar mulkin Jihar, harma ya bayyana irin nasarorin da ya samu a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa, da gina al’umma dama inganta tattalin arziƙi.
A ƙarshe sanarwar Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Ismaila Uba Misilli ya ce, Gwamnan ya gayawa Shugaba Tunibu yadda Gwamnonin Arewa maso gabas suka himmatu wajen kawo ƙarshen ƙalubalen rashin Wutar dake damun yankin.
Hafsat Ibrahim