Sanata Abubakar Kyari, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Arewa) ya zama shugaban riko na jam’iyyar ta kasa.
Hakan ya biyo bayan murabus din Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada, idan shugaban jam’iyyar na kasa ya yi murabus, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga shiyyar ne zai karbi ragamar mulki.
Kyari ya jagoranci wasu mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) zuwa wani taro da ke gudana a halin yanzu a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.
Wadanda suka shigo tare da Kyari sun hada da: Mataimakin Shugaban jam’iyyar ta Kasa (Kudu), Emma Enukwu; Mataimakin Shugaban Kasa (Arewa-Yamma), Salihu Lukman; Vice Chairman ta Kasa (Arewa-Gabas), Salihu Mustapha; Mataimakin Shugaban jam’yyar ta Kasa (Arewa Ta Tsakiya), Muazu Bawa; Mataimakin shugaban jam’yyar ta kasa (Kudu maso Yamma), Issacs Kekemeke; Mataimakin shugaban jam’yyar ta kasa (kudu-maso-gabas), Ejoroma Arodiogu da mataimakin sakataren kasa, Barr. Festus Fuanter.
Kyari, dan marigayi Birgediya Abba Kyari, tsohon shugaban mulkin soja na Arewa ta tsakiya daga 1967 zuwa 1975, an haife shi ne a ranar 15 ga Janairun 1960 a Jihar Borno.
Ya sami digiri na farko a 1986 daga Jami’ar Tennessee Martin da ke Amurka. Bayan haka a cikin 1989, ya halarci Jami’ar Webster St. Louis Missouri, Amurka don Jagoran Kasuwanci.
An zabe Kyari a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin rusasshiyar jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP) a shekarar 1998. Haka kuma, an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin rusasshiyar jam’iyyar All Peoples Party (APP) tsakanin 1999 zuwa 2003.
Daga 2003 zuwa 2005 da 2007 zuwa 2011, ya zama kwamishinan jihar Borno. A 2015, an zabe shi Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa a dandalin jam’iyyar APC. An sake zabe shi a 2019 kuma ya yi aiki har zuwa lokacin da aka nada shi mataimakin shugaban jam’yyar APC kasa a 2022.
Firdausi Musa Dantsoho