Zanga-zanga ta barke a Jihar Ogun saboda karancin Naira, An Kona bankuna

0
71

A wani karo, zanga-zanga ta barke a jihar Ogun kan karancin naira, inda faifan bidiyo a yanar gizo ke nuna yadda aka kona bankuna biyu a yankin Sagamu na jihar.

An tattaro cewa rikicin ya barke ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin sakamakon dakatar da ayyukan bankunan da Automated Teller Machines ATM da aka ce ba su ba da kudi ba tun makon jiya.

Hotunan bidiyo da aka yada a ranar Litinin sun nuna mazauna da dama suna kallo yayin da aka kona bankunan Keystone da Union tare da wasu matasa rike da katako don nuna adawa.

Tare da tashin gobara, masu zanga-zangar sun tare babbar hanyar Sagamu-Benin tare da hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa.

Akarigbo na Remo, Oba Babatunde Ajayi, ya yi kira da a kwantar da hankula.

Sanarwar da fadar ta fitar ta ce, “Ina kira ga kowa da kowa da su kwantar da hankalinsu da lumana yayin da muke ci gaba da kulla alaka da gwamnatin tarayya.

“Wannan manufar ba ta jiha ko karamar hukuma ba ce. Don haka, barnata rayuka da dukiyoyi za ta ƙara haifar da mummunan yanayi ne.

“Ina kira ga mutanenmu da su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi kamar yadda kotun koli ta yanke. Babu mutumin da in ya karɓi tsohon naira zai yi asara. Zan iya tabbatar muku da hakan, kuma don Allah ku yi riko da wannan alkawari.

“Bugu da ƙari, ina kuma ba wa dukan mutanen kasuwarmu umarni da su cigaba da karɓar tsofaffin takardun kudi. A nan na yi alkawarin cewa babu wanda zai yi asara don ya mallaki tsoffin kudi.”

A halin da ake ciki kuma, a ranar Alhamis din makon da ya gabata, shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a wani shirye-shirye na kasa, ya ce tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 ba su da wata doka a kasar, sai dai ya kara wa’adin tsohuwar Naira 200 na tsawon kwanaki 60, har zuwa 10 ga watan Afrilu, 2023.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho