Kamfen din Tinubu ya ki amincewa da Nadin Naja’atu Muhammad a matsayin Kodinetan PSC

0
90

 

Majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta yi watsi da nadin Naja’atu Muhammad a matsayin kodinetan hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta shiyyar Arewa maso Yamma.

 

News Point Nigeria ta ruwaito cewa, hukumar ta PSC ta nada Naja’atu, tsohuwar Darakta a hukumar kula da kungiyoyin farar hula na jam’iyyar APC PCC a matsayin daya daga cikin masu kula da yadda jami’an ‘yan sanda ke gudanar da zabukan na ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris.

 

Naja’atu ta fito karara ta caccaki mai rike da tutar jam’iyyar APC, Bola Tinubu bayan ta koma sansanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

 

Jam’iyyar APC PCC a cikin wata sanarwa da kakakin ta Festus Keyamo ya fitar a ranar Litinin, ta ce, “Bai kamata mu jaddada cewa aikin da aka baiwa Naja’atu na bukatar mutum mai gaskiya da rashin son zuciya da zai gudanar da aikin cikin himma ba tare da zargi ba. Al’umma ba za su samu haka daga Naja’atu ba.

 

“Don haka muna bukatar a gaggauta janye sunan Naja’atu Bala Muhammad a matsayin kodineta na hukumar ‘yan sanda a shiyyar Arewa maso Yamma ko kuma wani yanki a kan haka.

 

“Tana da ‘yancin ci gaba da yi wa duk wani dan takarar da take so kamfen kuma ta zabi dan takarar, amma ba za a iya ba ta rigar da za ta saka a wannan lokacin da ake nufi da tsaka tsaki kawai.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho