Zargin Cin Hanci: APC Ta Dakatar Da Shugabanta Na Ƙasa Ganduje

0
16

Shugabancin Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje, Wanda ya kasance Dan Mazaɓar Ganduje dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kanon Najeriya. Jam iyyar ta dakatar dashi a Nan take

Kasancewar shi Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, sanarwar hakan ta fito ne ta bakin me bawa Jam’iyyar Shawara akan fannin Shari’a a Mazaɓar Ganduje, Haladu Gwanjo a yayin taron manema labarai da suka gudanar a yau Litinin, inda ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.

Gwanjo ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon zargin da Gwamnatin Kano  take yi wa Gandujen na karɓar cin hanci da kuma karkatar da dukiyar Al’ummar Kano.

A ƙarshe Sanarwar ta ce sun ɗauki matakin ne, saboda yadda Gandujen ya gaza kare kansa akan tarin Zarge-zargen da ake yi masa.

 

 

Hafsat Ibrahim