Hukumar NDLEA ta Cafke wata mata mai ciki dauke da miyagun kwayoyi tare da kuma jabun kudi

0
18

*Hukumar NDLEA ta Cafke wata mata mai ciki dauke da miyagun kwayoyi tare da kuma jabun kud*

Daga Shamsiyya Hamza Sulaiman

 

Yayin da ya ke Karin haske babban Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi yace,

 

Jami’an sun cafke wata motar bas ta yan kasuwa dauke da jabun kudi naira miliyan 3.2 mallakin wasu mutane uku: Favour Peter mai dauke da ciki wata takwas, mai shekaru 24; Esther Adukwu, mai shekaru 27, da Ochigbo Michael, mai shekaru 39, wadanda aka kama a wurin shakatawa na Jabi da ke Abuja, a wani samame da aka yi a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu.

 

Hakan na faruwa ne a yayin da jami’an NDLEA tare da hadin gwiwar rundunar sojojin ruwa ta Najeriya ,suka kama Aliyu Lawal mai shekaru 37 a hanyar Lokoja zuwa Abuja a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu, inda suka kwato tabar wiwi 620 mai nauyin kilogiram 310.

 

A ranar Litinin 8 ga watan Afrilu jami’an NDLEA sun kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa a garin Bassey Edom da ke Calabar bisa laifin hadawa da siyar da wani sabon sinadari mai saurin kisa mai suna NPS a gidan ta. cakude da nau’ikan kayan maye daban-daban waɗanda ta ke bari su tsumu, a yayin kamata an kwato lita 18 na sinadarin mai hatsarin gaske a cikin bokitan fenti, matar ta yi ikirarin cewa ta fara samar da haramtattun magungunan ne tun a watan Oktoba 2023.

 

Haka zalika hukumar ta kama wasu mutane biyu: Sani Mohammed, mai shekaru 43, da Christopher Eze, mai shekaru 64, a unguwar Sabon Gari dake Kano a ranar Talata 9 ga watan Afrilu tare da kwato miyagun kwayoyi guda 900,000 daga hannunsu.

An kama akalla kilogiram 252 na tabar wiwi yayin wani samame da aka kai dajin Ijesa Isu, jihar Ekiti a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu yayin da wasu mutane hudu: Adamu Umar, mai shekaru 39; Abdullahi A Gimba, 27; Julius Uduakhomu, 28; sai Micheal Sunday, mai shekaru 24, suna cusa kilogiram 40 na haramtattun magungunana cikin injin wata motar iskar gas a kauyen Agho dake yankin Owan ta Gabas a jihar Edo. Kuma sun tabatar da cewa arewacin Nigeriya zasu kawo kayan

 

A jihar Ogun, an kama wani da ake zargi mai suna Ismaila Ogun a ranar Juma’a 12 ga watan Afrilu da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 79 a Imeko, yayin da aka kama wani matashi mai suna Friday Abah mai shekaru 18 da kilogiram 410 na tabar wiwin a lokacin da jami’an NDLEA suka kai farmaki sansanin Obatedo, dajin Itaogbolu, a karamar hukumar Akure ta Arewa. , Jihar Ondo.

 

Duba da irin kwazo gami da himamr hukumar ta NDLEA, tasa kungiyoyin da dama daukar aniya kirkiro da hanyoyin wayar da kan alummar kasa,wajan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya tun daga matakin gwamnati, jami’an tsaro da dai sauransu.

Daga karshe da ya yaba wa hafsoshi jihar Kogi, Cross River, Ondo, Ekiti, Ogun, Imo, Kano, da Edo na hukumar da kwamandojin hukumar bisa bajintar da suka yi wajen rage samar da miyagun kwayoyi a kasar nan, Shugaban Hukumar ta NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya kuma yaba wa da sauran takwarorinsu na fadin kasa baki daya.

 

 

 

Hafsat Ibrahim