Sa’o’i saba’in da biyu da fara yakin neman zaben 2023 a hukumance, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Bola Tinubu ya bace a fagen, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin magoya bayansa.
Tinubu dai ya bar kasar ne ba tare da sanarwa ba a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya tafi kasar Birtaniya, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa dan takarar zai je kasar Birtaniya ne domin duba lafiyar sa, duba da cewa ya shafe wasu watanni a kasar.
Ayo Ayelabowo, daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC Council, a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Arise TV, ya ce Tinubu na hutawa ne a Landan saboda mutane ba za su bari ya huta a Legas ko Abuja ba.
Yana Landan dalilin da yasa yake Landan shine bazai iya hutawa a Lagos ba, bazasu barshi ya huta ba. Wannan mutumin yana aiki kusan sa’o’i 20 a kowace rana. Sabida haka Mutane suka ce masa, yana buƙatar barin ƙasar nan, kuma yana buƙatar hutawa saboda yaƙin neman zaɓe na tafe. Mun yi tunanin zai iya hutawa a Abuja amma ba za su bar shi ba. Batun na yau shi ne gayyatar da aka yi masa na yarjejeniyar zaman lafiya ta zo a kurarren lokaci
A cikin satin nan ne dai labarin ina Tinubu yake? ya ke ta yaduwa na dan lokaci, yayin da ‘yan adawa suka yi wa tsohon gwamnan jihar Legas ba’a da cewa ya bar kasar a tsakiyar yakin neman zabe, inda suka yi nuni da zargin rashin lafiyar Tinubu.
A cikin magoya bayan jam’iyyar, musamman magoya bayan sa na yanar gizo, rashin gannin dan takarar a farkon yakin neman zabe ya sanya mutane da yawa cikin damuwa. Rashin halartar sa taro kan yarjejeniyar zaman lafiya da kwamitin zaman lafiya na kasa ya shirya ya sanya magoya bayansa cikin tsaka mai wuya.
‘Yan adawa sun yi tsokaci kan taron NBA, inda Tinubu bai samu halartar taron ba saboda yana kasar Birtaniya, ya bar abokin takararsa ya halarta.
Ko’odinetan babban birnin tarayya Abuja na Grassroot na Asiwaju, Abiodun Ibrahim, ya bayyana cewa samun lokacin hutu ba ya nuni da komai.
“Wannan zaben ba na wasu makonni ko kwanaki ba ne, watanni ne kawai. Asiwaju ya fara yakin neman zabe tun a watan Fabrairu. Ya yi nasara a firamare mafi wahala. A yayin gudanar da zabukan fidda gwani, ya ziyarci jihohi da dama a tarayyar kasar, inda ya yi taruka ba dare ba rana.”
Daga:Firdausi Musa Dantsoho