2023:Wike ya kuma gana da Peter Obi da Wasu Gabanin zaben 2023.

0
63

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake ganawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi. Haka kuma a taron da aka gudanar a daren ranar Litinin a gidan Wike da ke Fatakwal akwai tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko. Channels Television ta tattaro cewa shugaban na Rivers ya kuma gana da tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke; Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da dai sauransu.Ganawar ta Litinin da Obi na zuwa ne bayan Wike ya gana da dan takarar shugaban kasa na LP. Kamar dai taron da ya gabata, ko daya daga cikin ‘yan siyasa bai bayyana dalilin da ya sa aka yi taron na baya-bayan nan ba. Hakazalika, Mimiko ya gana da Wike a karshe a gidansa da ke Fatakwal a ranar Alhamis, 11 ga watan Agusta. Gwamnan Ribas yana ganawa da manyan ‘yan siyasa a baya-bayan nan, musamman wadanda suka fito daga wasu bangarorin siyasa. Ya rika karbar manyan jiga-jigan siyasa, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa zai iya ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan ya kasa cin tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar. Duk da cewa Wike ya sha yin alkawarin yin biyayya ga babbar jam’iyyar adawa, harshen jikinsa na nuni da cewa ba zai yi wa Atiku Abubakar aiki ba, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023.

UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.