‘Yan sanda sun fatattaki ‘yan ta’adda a Katsina, sun kwato dabbobi

0
54

Ana fargabar an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da raunata wasu da dama bayan da wata tawagar jami’an ‘yan sanda suka dakile harin da suka kai a kauyukan Dadawa da Barkiya da ke karamar hukumar Kurfi a jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, yayin da ‘yan ta’addan suka yi kazamin artabu da ‘yan ta’addan, sun samu nasarar kwato tumaki 74, awaki 34 da kuma shanu biyu. 

Rundunar ‘yan sandan ta samu kiran waya da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Litinin cewa ‘yan ta’addar da yawansu ya kai 80 a kan babura dauke da manyan muggan makamai, sun kai hari a kauyukan biyu a lokaci guda. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, bayan samun labarin, rundunar ta tura dakarun ta zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar. 

Ya ce har yanzu tawagar ‘yan sanda na ci gaba da sintiri a yankin da nufin kamo ‘yan ta’addan da suka raunata tare da kwato gawarwakinsu.

A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Idrisu Dabban Dauda ya yaba da kokarin da jami’an suka yi na dakile ‘yan ta’addan.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake fama da ‘yan ta’adda a jihar.

 Daga Firdausi Musa Dantsoho