2024: Gwamnan Gombe Ya Yafewa Fursunoni 39, Tare Da Ayyana Shirin Sake Raba Tallafi

0
17

2024: Gwamnan Gombe Ya Yafewa Fursunoni

Daga Yunusa Isa, Gombe

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi afuwa ga fursunoni 39 dake tsare a gidajen kaso daban-daban na fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na sabuwar shekara da aka watsa kai tsaye ga al’ummar jihar, ta gidajen rediyo da shafukan sada zumunta.

Gwamnnan Yace an saki 26 daga cikin fursunonin 39 ne ba tare da wani sharaɗi ba, yayin da aka ragewa sauran 13n wa’adin zamansu a gidan yari.

Yace an ɗauki matakin ne don murnar sabuwar shekara kamar yadda majalisar bada shawara kan afuwa da jinƙai ta jihar ta bayar.

Gwamnan ya yi fatan waɗanda aka yiwa afuwar za su zama mutanen kwarai tare da zama jakadu nagari a cikin al’umma.

A ɗaya ɓangaren kuma, Gwamna Inuwa Yahaya, yace duba da irin mawuyacin halin da tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan biyo bayan cire tallafin man fetur, a yau Talata gwamnatinsa za ta ƙaddamar da rukuni na biyu don rage raɗaɗin halin da ake ciki, don daƙile illolin da magidanta marassa galihu ke ciki.

Yace a sabon rukunin tallafin, ana sa ran fiye da mutane 90,000 ne za su ci gajiyar kayan abinci da za a raba a faɗin jihar.

Da yake taya murna ga al’ummar jihar da ƴan Najeriya bisa shiga sabuwar shekarar, Gwamnan ya buƙacesu su ƙara jajircewa, da yin addu’oi dama bada goyon baya ga hukumomi don inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.

Gwamna Inuwa ya bada tabbacin ci gaba da jajircewar gwamnatinsa wajen samar da ƙarin romon demokraɗiyya don inganta rayuwar al’ummar jihar.

Ya kuma godewa Allah Maɗaukakin Sarki da ya kawo mu shekarar ta 2024 cikin rai da ƙoshin lafiya, yana mai fatan cewa shekarar za ta kasance mai cike da kwanciyar hankali da wadata ga al’ummar Jihar Gombe da Nijeriya.