Jirgin fasinjojin Japan Airlines ya kama da wuta bayan da yayi karo da Jirgin jigila.
Jirgin saman Japan ya yi karo da na jigilar kaya,Wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane 5 a lokacin da jirgin saman kasar Japan ya afkawa wani jirgin da ke jigilar kayan agaji a lokacin da ya le sauka a filin jirgin saman Haneda na birnin Tokyo, lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda nan take wuta ta kama.
Bidiyon da aka wallafa a intanet masu ban mamaki sun nuna lokacin da jirgin ke sauka ƙasa kuma ya faɗa wa jirgin hukumar Coast Guard mai kula da gaɓar tekun ƙasar wanda ke dauke da kayan agaji Al ummar da girgizar kasar jiya ta shafa. Hatsarin ya faru da misalin karfe 5:55 na yamma a agogon ƙasar.
Jirgin saman mai lamba 516, samfurin Airbus A350 ya taso ne daga New Chitose Airport a tsibirin Hokkaido zuwa filin jirgin saman Haneda na birnin Tokyo, a cewar tashar talabijin ta NHK ta Japan.
Mutum daya ne kawai ya tsira a cikin jirgin ,Wanda daya da ke ɗauke da kayan agajin. Jami’an kashe gobarar na kwana-kwana sun bayyana cewar ana kyautata zaton an kwashe dukkan fasinjojin 400 daga cikin jirgin fasinjan Wanda shi ya janyo hatsarin.
Hafsat Ibrahim