Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta labarin da ake yadawa musamman a kafafen sadarwar zamani na ‘social media’ cewa an sauya sunan jihar daga Kaduna zuwa jihar Zazzau.
A cikin wata sanarwa da DCL Hausa ta samu daga mai taimaka wa Gwamna El-rufa’i kan harkokin sadarwa Muyiwa Adekeye, ta ce mutane ne ke karar da labarin kanzon kurege.
Sanarwar ta ce labarin babu shi, babu alamar shi. Har ma sanarwar ta kira labarin da kirkirarre.
“Ba a sauya wa jihar Kaduna suna ba. Ku yi watsi da wannan kirkirarrwn labarin da ke yawo. Ba na gaskiya bane. Inji sanarwar”.
A daren Lahadi wayewar Litinin dai ne aka samu a kafafen sadarwar zamani cewa an sauya sunan jihar Kaduna zuwa jihar Zazzau bayan kudirin da ‘yan majalisar dokokin Nijeriya daga jihar Kaduna suka gabatar a zauren majalisar dokoki ta kasa.
Daga Fatima Abubakar.