Rawaitowa Daga Adam Muhammad Bichi
Babbar Sakatariyar Hukumar Dakta Rahila Mukhtar ce ta bayyana hakan yayin wata ziyarar wayar da kai da wasu kungiyoyi ƙarƙashin jagorancin Sunusi Hashim suka kai.
Dakta Rahila ta ce hukumar ta riga ta shigar da masu ɗauke da cutar HIV cikin tsarin kula da lafiyar jihar, tana mai cewa yanzu haka marasa lafiyar tarin fuka ma za su amfana da irin wannan tsarin kula da lafiya ƙarƙashin shirin masu rauni.
A cewarta, cutar tarin fuka na ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma wadda ke buƙatar kulawa cikin gaggawa da kuma haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da marasa lafiya sun samu kulawa da tallafin da ya dace.
Ta bayyana cewa shigar da marasa lafiyar tarin fuka cikin tsarin inshorar lafiya zai taimaka wajen rage matsalolin kuɗaɗen jinya tare da inganta samun damar gwaje-gwaje, magunguna da sauran muhimman hanyoyin kula da lafiya.
Dakta Rahila ta kuma sake jaddada ƙudirin hukumar na tallafa wa al’umma masu rauni a faɗin jihar ta hanyar shirye-shiryen kiwon lafiya.
S nasa jawabin, Jagoran Kungiyoyin Sunusi Hashim, ya yaba wa hukumar bisa ƙoƙarin da take yi wajen inganta walwalar marasa lafiyar tarin fuka a jihar.
Ya bayyana shirin shigar da marasa lafiyar cikin tsarin a matsayin babban mataki wajen ƙarfafa yaƙi da cutar tarin fuka da kuma rage wahalhalun da marasa lafiya ke fuskanta, musamman masu ƙaramin ƙarfi da iyalai masu rauni.
Sunusi ya kuma yi kira da a ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, abokan hulɗar ci gaba da ƙungiyoyin farar hula domin yaƙi da cutar tarin fuka da sauran cututtuka masu yaɗuwa a faɗin jihar Kano.
Wallafawa Hafsat Ibrahim kawo

Hukumar Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta sanar da shirin shigar da cutar tarin fuka 6,000 cikin tsarin kula da lafiya na masu rauni, a wani yunƙuri na ƙarfafa samun kulawa da rage yawaitar cutar a jihar Kano.
