MAGOYA BAYAN ADC A KARAMAR HUKUMAR NASARAWA SUN YABAWA SHUGABANNIN JAM’IYYA KAN ADALCI DA BIN DOKA

0
17

Magoya bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Karamar Hukumar Nasarawa sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shugabannin jam’iyyar bisa yadda suka gudanar da zaɓen fidda gwani cikin lumana, adalci da bin kundin tsarin jam’iyyar.

 

Magoya bayan sun ce hukuncin da jam’iyyar ta yanke na tsayar da Hon. Sa’id Ibrahim Nakowa a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Nasarawa ya biyo bayan tsarin dimokuraɗiyya da dokokin jam’iyyar, saboda haka ya dace a mutunta shi tare da haɗa kai domin samun nasara a babban zaɓe.

 

Sun bayyana cewa dimokuraɗiyya tana ƙarfafuwa ne idan aka mutunta sakamakon tsarin da aka amince da shi, tare da fifita haɗin kai da ci gaban jam’iyya fiye da son rai ko bambancin ra’ayi.

 

Magoya bayan sun kuma yaba wa dukkan ‘yan takarar da suka shiga zaɓen fidda gwani saboda nuna kishin jam’iyya da bayar da kansu domin yi wa al’umma hidima. Sun yi kira gare su da magoya bayansu da su rungumi sakamakon da aka samu tare da ba zaɓaɓɓen ɗan takara cikakken goyon baya, domin samun nasarar jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027.

 

A cewarsu, Hon. Sa’id Ibrahim Nakowa ya gabatar da manufofi masu ma’ana da tsari na ci gaban Karamar Hukumar Nasarawa, waɗanda suka mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, ilimi, lafiya, ƙarfafa mata da matasa, tsaro, bunƙasa kasuwanci da inganta rayuwar al’umma.

 

Sun yi addu’ar Allah Ya ƙara bai wa shugabannin jam’iyyar hikima da adalci, Ya haɗa zukatan dukkan mambobin ADC, Ya kuma ba su nasarar kawo sauyi mai amfani ga Karamar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

 

— Magoya Bayan Hon. Sa’id Ibrahim Nakowa

ADC, Karamar Hukumar Nasarawa