JAHAR GOMBE YA KARBI BAKONCIN MASU RUWA DA TSAKI,YAYIN DA GWAMNA INUWA YAHAYA YA AURAR DA DAN SA.

0
207

A jiya ne jahar Gombe ta karbi bakwancin manya manya wakilan Gwamnati, masu rike da madafun iko,Masu ruwa da tsaki,manyan attajiai da Malaman addini wurin daurin dan Gwamnan jahar,Gwamna Inuwa Yahaya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne  ya Jagoranci Tawagar Buhari Yayin Da Tinubu, Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa, Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Gwamnoni 8, Mambobin NASS, Ministoci, Da Sauransu Suka shiga Garin na kawa wato Gombe Jewel.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi matukar farin ciki yayin karbar bakoncin abokan arziki zuwaGombe domin halartar daurin auren dansa, Arc Misbahu Inuwa Yahaya wanda aka  daura aurensa da mai masoyiyar sa,, Barista Amina (Ameera) Babayo.

Babban limamin masallacin Gombe ta tsakiya Sheikh Barista Ali Hammari ne ya jagoranci daurin auren Fatiha tsakanin Misbahu da Ameera.

Mai Martaba Sarkin Gombe, Dr Abubakar Shehu Abubakar III ya tsaya a matsayin wakilin ango (Wakil) yayin da Alhaji Kawu Adamu Dan Malikin Gombe ya kasance waliyin amarya ( Waliy).

Waliyyin Amarya, Alhaji Kawu Adamu ya aura Ameera ga Arch Misbahu Inuwa Yahaya ta hannun Wakilinsa, Sarkin Gombe wanda Babban Hakimin Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar ya wakilta biyo bayan  daurin auren da kuma shelanta Naira Dubu Dari. a matsayin sadaki.

Shaidan Daurin auren da aka gudanar a babban masallacin garin Gombe ya samu halarcin manya manyan baki da masu fatan alheri. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha. Sauran manyan baki da suka halarci bikin sun hada da: Jam’iin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, abokin takararsa, Sen. Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sen. Abdullahi Adamu, mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnonin Progressives, Sen. Atiku Bagudu, gwamnonin Arewa maso Gabashin Adamawa, Rt Hon Ahmadu Umaru Fintiri, Borno; Farfesa Babagana Umara Zulum, Bauchi; Abdulkadir Bala Mohammed da Yobe; Hon Mai Mala Buni da kuma Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.

Sauran mutanen da suka halarci taron, sun hada da tsohon gwamnan jihar Gombe, Sen. Muhammad Danjuma Goje, tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Saudu Ahmed Alkali, Gobir, ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami. Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, tsohon ministan babban birnin tarayya Dr Aliyu Modibbo Umar da Sheikh Sani Yahaya Jingir fitaccen malamin addinin musulunci kuma shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatisunnah na kasa wanda Ash- Sheikh Ismaila Idris ya kafa. Tsohon ’yan takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP, Dakta Jamilu Ishiyaku Gwamna da kuma Dakta Babayo Ardo su ma su  halarci taron.

Bikin  ya kuma janyo hankulan ‘yan kasuwa da manyan ‘yan siyasa, sarakuna da abokan arziki da kuma dangin ango da na amarya da sauran su.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Babban Alkalin Alkalai, Babban Alkali, Khadi da Alkalai, Mambobin Majalisar Zartaswa na Jihar Gombe karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi da Shugaban Ma’aikata na Majalisar Dokokin Jihar Gombe Abubakar Inuwa Kari sun halarci taron,domin shaida bikin daurin aure mai dimbin tarihi.

Da yake jawabi a wajen liyafar karrama baki da aka gudanar a dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana irin soyayyar da bakin da suka nuna masa a matsayin abin da ya wuce gona da iri, inda ya ce taron wani lamari ne na musamman wanda ya ba shi damar shaida yadda dansa ya shiga. wani sabon lokaci na rayuwar sa.

Yayin da yake jinjinawa bakin da suka halarci taron, gwamnan ya kara da cewa kasancewarsu ya kara wa daurin auren armashi.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima da kuma shugaban majalisar  sun ba da sakon fatan alkhairi.

Daga Fatima Abubakar.