Korarren shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar da biyansa kudi N5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar Kano.
Rimingado ya tabbatar da karbar kudin a ranar Alhamis, inda ya ce zai bayar da wani bangare na kudaden ne ga sadaka.
A ranar Talata, Kotun Masana’antu ta kasa, Abuja ta umarci GTBank ya biya Mista Rimingado bashin albashin da ya tara daga asusun gwamnatin jihar, biyo bayan dakatarwar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa ba bisa ka’ida ba a watan Yulin 2021.
Idan dai zaku iya tunawa gwamnan ya dakatar da Mista Rimingado ne bayan ya bude bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan.
A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talata, bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar rantsuwa cewa gwamnatin jihar Kano ta na da asusun ajiyar banki da jimillar kudaden da ya kai N5,713,891.22 kasancewar an toshe hukuncin da aka yanke kan lamarin. a cikin asusun.
Da yake bayar da cikakken umarnin, Mai shari’a O.O Oyewumi ya umarci GTBank ya biya kudin a asusun Mista Muhuyi Magaji Rimingado cikin sa’o’i 48.
A cewar DAILY NIGERIAN, an bayar da umarnin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen mutunta hukuncin da kotun ta yanke a ranar 14 ga watan Disamba, 2022, da bayar da umarnin biyan da kuma amincewa da Mista Rimingado a matsayin kwararren shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Firdausi Musa Dantsoho