6Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wasu fitattun jaruman Kannywood guda biyu, Amina Uba Hassan da Adam Garba da aka fi sani da Raba Gardama, daga gudanar da harkokin fim a jihar har na tsawon shekara ɗaya.
Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan bayyanar jaruman a wani bidiyo da ta ce ya saɓa da tarbiyya kuma ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar jihar Kano.
Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a safiyar Lahadi, ya ce dakatarwar na cikin ƙoƙarin tsaftace tarbiyya da tabbatar da bin dokokin hukumar a masana’antar Kannywood.
Sanarwar ta ƙara da cewa dokar hukumar ta bai wa hukumar ikon dakatar da duk wani ɗan masana’antar fim da ya karya ƙa’idojinta, tare da gargadin cewa karya umarnin dakatarwar na iya jawo hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.
Da yake jawabi kan lamarin, shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya yi kira ga jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood da su guji duk wani abu da ka iya zubar da mutuncin masana’antar ko kawo mata rashin kima a idon al’umma.
Hukumar ta kuma buƙaci producers da directors na masana’antar Kannywood da su mutunta umarnin dakatarwar, tana mai cewa yin watsi da shi tamkar ƙalubalantar dokar hukumar ne kai tsaye




