Sakatare na dindindin na babban birnin tarayya Mista Olusade Adesola ya yi kira ga ma’aikata da su tabbatar da cewa gaskiya da rikon amana ya ci gaba a dukkan matakai.
Mista Olusade ya bayar da wannan umarni a lokacin bikin karrama ma’aikatan gudanarwar guda goma da suka yi ritaya a karshen mako a Abuja.
Ya bayyana cewa idan ba tare da biyayya, sadaukarwa da kuma rikon amana ba zai yi wahala kowane tsari ya yi kyau.
Don haka Adesola, ya ja hankalin wadanda har yanzu suke aiki da su yi koyi da salon rayuwar wadanda suka yi ritaya, wanda ya ce hakan ya taimaka ba kadan ba wajen samun nasarar hukumar babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce: “Ga wadanda suke cikin hidima, na yi imanin akwai kyawawan halaye da da’a da za mu yi koyi da su daga manyan ’yan uwanmu da suka fice, duk da cewa za ku ci gaba da tabbatar da aiki tukuru, da gaskiya, rikon amana, ssadaukarwa tukuru wurin gudanar da Sabis.
Sakataren din din ya bukaci ma’aikatan sakatariya, sassan da hukumomi (SDAs) da su yi kokarin aiwatar da ayyukan gwamnati a cikin kyakkyawan yanayi.
“Ga wadanda suka yi ritaya na musamman, bai kamata su ga yin ritaya daga aiki ya zama marar amfani da kashewa ba. Sai dai don cin gajiyar gaskiyar cewa yanzu kuna da iko akan lokacinku, don haka, yanzu kuna iya ba da ƙarfin ku don shiga cikin sauran fannoni. na mafi girman cikawa da nasara a rayuwa.
“Babban abin farin ciki da gamsuwa shi ne yadda abokan aikinmu da suka yi ritaya suka yi hidima mai inganci ga Hukumar FCT da sauran jama’a a tsawon wadannan shekaru masu yawa, gwamnatin tana alfahari da ku kuma za ta yi alfahari da ku.”
A nasa bangaren, daraktan kula da harkokin ma’aikataikan babban birnin tarayya Abuja Malam Muhammed Bashir ya yi alkawarin shirin gwamnatin na ci gaba da samar da kayan aiki ga ma’aikatanta domin samun kyakkyawan aiki.
A nata jawabin, shugabar kwamitin shirya taron kuma mukaddashiyar darakta na FCT Reformed Coordination and Improvement Department, Dr Jumai Ahmadu ta ce wannan liyafar cin abincin wata alama ce ta karramawa bisa irin gudunmawar da ‘yan fansho ke bayarwa ga gwamnati.
A cewarta, wannan ra’ayin zai taimaka matuka wajen karfafa wa wadanda ke aiki kwarin guiwa da su yi iya kokarinsu na gudanar da harkokin gudanarwar babban birnin tarayya Abuja
Ma’aikatan gudanarwa guda goma na FCTA/FCDA da suka yi ritaya daga Janairu zuwa Maris, 2023 sun hada da Okeke Ifeoma Ebele Sakatariyar Noma da Raya Karkara, Okonkwo Emmanuel Obi Sashen Tsare Tsaren Tattalin Arziki, Danazumi Anthony Sarkin-Noma, Hukumar Kare Muhalli ta Abuja.
Sauran sun hada da Saka Isiaka Ahmed Federal Capital Development Authority (FCDA), Baffa Isa Muhammad Abuja Hukumar Kare Muhalli, Sulaiman Mohammed Sulaiman FCDA, Dr Iwere Ejemai Vincent FCT Sakatariyar Lafiya da Ayyukan Jama’a.
Usman Yahaya Musa Babban Sakatariyar Sufuri na FCT, Perpetua N. Ohammah FCDA da Elizabeth Ukamak Atang Sashen Fansho na Babban Birnin Tarayya.
Daga Fatima Abubakar.