Gbajabiamila yayi murabus daga matsayin shugaban majalisar wakilai

0
35

TSOHON Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila ya yi murabus daga Majalisar Wakilai domin ya ci gaba da aikinsa na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

An gabatar da takardar murabus din nasa ne a harabar majalisar inda kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya karanta.

Tashar talabijin ta Channels a ranar Laraba ta bayar da rahoton cewa, Gbajabiamila zai sauka daga mulki, domin samun damar mayar da hankali kan ayyukan da ke gabansa a cikin sabuwar gwamnati.

An fara nuna damuwa kan yadda zai gudanar da ayyukan biyu ganin cewa an kaddamar da tsohon shugaban majalisar tare da takwaransa a ranar Talata kuma ya zabi shugabancin majalisar.

Sai dai a yanzu dan majalisar da ke wakiltar Surulere 1 ya mika takardar murabus dinsa kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sake gudanar da sabon zabe domin cike gurbin.

Firdausi Musa Dantsoho