Gwamnatin Legas ta yi karin haske game da binne mutane 103 da ENDSARS ta shafa

0
17

 

Gwamnatin jihar Legas ta yi martani kan wata takarda da aka wallafa da ke nuna amincewarta da N61,285,000 don gudanar da jana’izar mutane 103 da aka bayyana a matsayin wadanda aka kashe a karshen shekarar 2020 ta EndSARS, tare da tabbatar da cewa wadanda za a binne ba daga harbin Lekki Tollgate ne da ya janyo cece-kuce ba.

Takardar mai dauke da kwanan watan 19 ga Yuli, 2023, na daukar matakai na sarrafa kudaden bayan amincewar da gwamnan ya yi, ta bayyana a shafukan sada zumunta da safiyar Lahadi, lamarin da ya harzuka.

Babban sakataren ma’aikatar lafiya, Dakta Olusegun Ogboye, ya tabbatar da wasikar a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Lahadin da ta gabata, sai dai ya dage cewa an wallafa bayyanan ba daidai ba.

Jami’in gwamnatin ya musanta cewa wadanda abin ya shafa sun fito ne daga tashe-tashen hankula da suka faru bayan zanga-zangar EndSARS.

Ogboye ya ce Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Legas (SEHMU) ta tsinci gawarwaki a sakamakon rikicin #EndSARS da rikicin al’umma.

Yankunan da aka ambato sun hada da Fagba, Ketu, Ikorodu, Orile, Ajegunle, Abule-Egba, Ikeja, Ojota, Ekoro, Ogba, Isolo da Ajah na jihar Legas. Ogboye ya kara da cewa an kuma samu fasa gidan yari na gidan yarin Ikoyi.

“Wadanda aka kashe 103 da aka ambata a cikin takardar sun fito ne daga wadannan abubuwan ba kuma ba daga Lekki Toll-gate ba kamar yadda ake zargi. Don kaucewa shakku, ba a samo wani gawa daga lamarin Lekki Toll Gate ba, “in ji sanarwar.

Firdausi Musa Dantsoho