Ministan Tsaro, Mohammed Bello Matawalle ya yi Allah wadai da sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara.
Matawalle yayin da ya yi Allah wadai da wannan aika-aika, ya kuma jajanta wa iyaye, al’ummar malamai, da daukacin al’ummar Jihar Zamfara bisa wannan mugun sace-sacen da aka yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Attari M. Hope, Ag. Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya, ya fitar a ranar Lahadi, a Abuja.
Sanarwar ta ce: Ina taya ku jin radadin kuma ina yin Allah wadai da wannan mummunan aiki da ake zargin ‘yan fashi ne suka aikata.
Yayin da ya yi Allah wadai da harin baki daya, ya kuma yi kira ga jami’an tsaron kasar da suka sadaukar da kansu da su kara kaimi tare da samar da duk wata hanya da ta dace domin ganin an dawo da daliban da aka sace.
Ya ce dole ne kowa ya tashi tsaye domin ganin an sako daliban da aka sace.
“A tsarin shugaban kasa Ahmed Bola Tinibu mai lamba takwas na karfafa tsaron kasa don samar da zaman lafiya da wadata, na yi Allah wadai tare da shan alwashin ganin an sako daliban da aka sace.
Da yake tabbatar wa al’ummar jihar, Matawalle ya ce, an riga an jibge sassan sojoji na sama da na kasa a cikin jihar domin za a dauki kowane mataki na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya baki daya.
Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasar kudurin Gwamnatin Tarayya na samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Firdausi Musa Dantsoho