Yanzu Yanzu: Gobara Ta Lalata Wani Sashin Kotun Koli

0
12

Kotun ta ce wani sashe na kotun kolin ya ci wuta a safiyar ranar Litinin, duk da cewa ba a sami asarar rai ba.

Jami’in hulda da jama’a na kotun, Mista Festus Akande, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce musabbabin gobarar wutar lantarki ce daga daya daga cikin kotunan alkalai kuma an kashe su ne ta hanyar amfani da na’urorin kashe gobara.

Akande ya kara da cewa labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa an samu asarar rayuka “labari na karya ne”.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safe.

An tattaro cewa masu aikin shara da ke bakin aiki da wasu ma’aikatan da suka shiga ofis da wuri ne suka gan gobarar tare da tayar da kura.

An ce ma’aikatan sun yi amfani da na’urorin kashe gobarar da ke ginin wajen yakar gobarar.

Gobarar ta kama ofisoshi uku ciki har da na Mai shari’a Mohammed Saulawa.

Firdausi Musa Dantsoho