DA DUMI-DUMI
Gwamnan Kano ya tabbatar da nadin Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Gwamnan Kano, ya ba tsoffin sarakuna Sa’o’i 48 su fice da masarautun.
Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya maida Sarki Sunusi na biyu kan kujerar Sarkin Kano a matsayin Sarki na 16.
Gwamnan ya mayar da sunusi lamido sunusi a matsayin sarkin kano
yayin da ya bai wa Sarakunan da aka sauke wa’adin awanni 48 su bar gidajen Gwamnati su kuma mika kundin bayanin barin kujerunsu ga Kwamishinan Kananan Hukumomi.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin taron manema labaran da yake gudanarwa yanzu haka a fadar Gwamnatin Kano.
Kuma matakin yazo ne bayan Majalisar dokokin Kano ta rushe dukkan masarautun biyar da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙiraa a Shekarar 2019….
Ana saran Dambarwar Sarautar Kano tazo karshe Gwamna Abba kabir ya Dawo da Muhammadu Sunusi Sarkin Kano.
Daga karshe dai an umarci tsofaffin Sarakuna dasu fice daga masaurautun da suke ciki, ba tare da bata lokaci ba.
Hafsat Ibrahim