Hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kai farmaki fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a daidai lokacin da jita-jitar tsige Sarkin ta yi katutu.
Rahotanni na nuni da cewa an jibge jami’an Hukumar DSS a fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayaro.
Bayan yi wa dokar da ta samar da sabbin masarautu a jihar tare da rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.
Wannan na zuwa ne bayan zama da majalisar ta yi a yau Alhamis tare da yin duba a kan dokar da ta kirkiro sabbin masarautun.
Tun da farko tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya yi amfani da dokar wajen tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14 a 2020.
Shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar Dala, Hussien Dala ne, ya gabatar da kudirin gyara dokar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Sai dai an wayi gari babu sarki mai ci a Jihar Kano bayan majalisar dokoki ta tsige sarakunan Kano, Bauchi, Gaya, Karaye da kuma Rano.
Hafsat Ibrahim