A YAU JAM’IYYAR MAI MULKI KE GUDANAR DA BABBAN TARON TA NA KASA A EAGLE SQUARE.

0
72

A yau asabar 26 ga watan maris 2022 ne Jamm’iyar da ke mulki APC ke gudanar da babban taron ta na kasa.

Yan taka shida masu neman kujerar shugabancin fatin sun janye  wa Abdullahi Adamu domin mara wa shugaba Buhari baya wanda ya nuna ra’ayin sa akan tsohon Gwamnar jahar Nasarawa kuma Dan majalisar dattawa mai ci.

Hakan na kunshe ne a wata wasika da ke dauke  da sa hannun Senator George Akume na jahar Benue wanda shima yana cikin masu son kujerar.

An dai samu hargitsi da cunkoson jama’a yayin shiga Eagle Square inda ake kaddamar da taron,inda jami’an yan sanda suka fesa barkonon tsohuwa inda ya tarwatsa jama’a yayin da wasu suka yi asarar kayayyakinsu masu mahimmanci kamar su wayoyin hannu da kyamarori.

By Fatima Abubakar.