Kungiyar daliban Najeriya ta yi umurni ga daliban Najeriya da su fito kan tituna domin nuna damuwar su.

0
38

Kungiyar daliban Najeriya ta kasa a ranar Juma’a ta umurci dalibai da su mamaye titunan Abuja da tukwanen dafa abinci, katifunsu, da sauran illolinsu na kashin kansu domin nuna adawa da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara.

Shugaban NANS Sunday Asefon ne ya bayyana haka a wata wasika da ya aikewa shugabannin kungiyar na shiyyar.

An yi wa wasikar taken, ‘Sanarwar Gaggawa Kan Fara Tattaunawar Gaggawa da kwanan wata 25 ga Maris, 2022.

ASUU, a ranar 14 ga Maris, a karshen yajin aikin gargadi na makwanni hudu da ta ayyana a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta tsawaita shi da makwanni takwas kafin cimma yarjejeniyar ta da Gwamnatin Tarayya.

By Fatima Abubakar.