Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar murabus dinsa a daren jiya,kamar yadda muka samu rahoto.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a watan Maris din shekarar 2022, ya aike da takardar murabus dinsa zuwa fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja gabanin dawowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu daga taron kungiyar tarayyar Afrika (AU)da akayi a Kenya.
Daya daga cikin majiyar ta ce Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya aika wasikar murabus din ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
“Ya yi murabus. An aika da takardar murabus din da ya sanya wa hannu zuwa fadar shugaban kasa. Wasikar da aka aika wa shugaba Tinubu. Amma tun da shugaban kasar ya tafi Kenya don halartar taron kungiyar AU, an aike da wasikar zuwa ga shugaban ma’aikatansa,” inji majiyar.
Hakazalika, wata majiya ta kusa da Adamu ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa, “Shugaban ya yi murabus ne biyo bayan gungun jama’a da ke kusa da shugaban kasar suka hada kai domin kunyata shi a taron jam’iyyar da za a yi a gobe da ranar Laraba.”
Sai dai majiyar ta musanta wani rahoto da ke cewa shugaba Tinubu ne ya bukaci Adamu ya yi murabus gabanin taron majalisar zartarwa na jam’iyyar na kasa da za a yi gobe da Laraba. Jam’iyyar ta tsayar da ranakun 10 da 11 ga watan Yuli domin gudanar da tarukan kwamitin ta na kasa da na NEC domin warware matsalolin da suka shafe ta da kuma rikicin da ke tsakanin kwamitin ayyuka na kasa (NWC).
Sai dai daga baya an dage tarukan tare da dage zaman gobe da Laraba.
Wani dan jam’iyyar da ya aka kafa jam’iyyar da shi ya ce Adamu ya yi murabus ne a lokacin da ya samu labarin cewa wasu mutane biyu masu fada a ji kuma na kusa da shugaban kasar sun hada gungumin mutane don yin masa zanga-zanga kafin tarukan.
“Ya yi murabus ne saboda sun fara hada hannu don tsige shi a tarurruka masu zuwa. Ya yi murabus ne domin ya ceci kansa daga wulakanci,” in ji babban dan siyasar.
Da aka tuntubi Adamu, ya shaida cewa ba zai ce uffan ba kan lamarin har sai Shugaba Tinubu ya dawo daga taron AU.
“Ba zan yi magana a kan batun ba saboda shugaban kasa ba ya nan,” in ji Adamu wanda shi ne dan takarar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben kujerar shugaban kasa.
Idan dai ba a manta ba Adamu gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ayyana tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Wannan furuci da Adamu ya yi ya haifar da hargitsi a cikin jam’iyyar yayin da gwamnonin jam’iyyar daga Arewa suka yi masa kawanya. Sai suka je villa suka ce za a sanya shugaban kasa shiyyar Kudu.
Matsayin gwamnonin ya tilastawa jam’iyyar bude gasar neman tikitin takarar shugaban kasa. Tinubu ne ya lashe zaben. A kwanakin baya ne Adamu ya caccaki jerin sunayen manyan jami’an jam’iyyar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar, Tajudeen Abbas suka bayyana.
Firdausi Musa Dantsoho