Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Binciken Kisan Hakimin Kauye Da ‘Yan Bindiga Suka Yi

0
18

 


Gwamnatin Katsina ta kafa wani kwamiti da zai binciki kisan hakimin kauyen Dabaibayawa da ke karamar hukumar Batagarawa a jihar.

Isah Miqdad, mai taimaka wa Gwamna Dikko Radda ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Katsina, inda ya ce lamarin ya faru ne kimanin makonni biyu da suka gabata.

“Gwamnati ta fusata da yadda aka yi garkuwa da Hakimin Kauyen Dabaibayawa da kuma kisan gillar da aka yi masa, gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin.

 

“Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Malam Faruk Lawal-Jobe,” a cewar Mista Miqdad.

 

Da yake kaddamar da kwamitin a ranar Alhamis, mataimakin gwamnan ya umarce su da su binciki garkuwan da aka yi da hakimin kauyen, tare da zakulo wadanda suka aikata laifin.

Mataimakin gwamnan ya ce kwamitin ya kunshi wakilan ‘yan sanda, hukumar tsaro ta jiha, da kuma hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC).

Sauran sun fito ne daga ma’aikatar shari’a, kananan hukumomi da masarautu, da kuma masarautar Katsina.

 

Ya kuma bayyana cewa kwamitin yana da makonni biyu wanda zai gabatar da rahotonsa domin tantancewa daga baya

Majalisar Masarautar Katsina ta godewa gwamnan bisa kafa kwamitin tare da bada tabbacin goyon bayansa domin cimma manufofin kafa kwamitin.

 

Firdausi Musa Dantsoho