Al’adun wasu kabilu guda bakwai masu ban mamaki a fadin nahiyar Afirka

0
695

 Al’ummomin wadannan ƙabilun suna yin wasu al’adu masu ban mamaki.

Nahiyar Afirka na cike da ayyuka masu ban mamaki da wasu aka san su, wasu da yawa kuma duniya ba ta sani ba.

Wasu daga cikin waɗannan al’adu masu ban mamaki har yanzu suna nan shekaru da yawa bayan wayewa.  Waɗannan al’ummomin ƙabilun suna yin wasu al’adu waɗanda za su firgita ku.

  1.  Al,adan Satar matan juna – Nijar

 A kabilar Wodaabe ta Nijar da ke yammacin Afirka, an san maza na satar matan juna.  Auren farko na Wodaabe iyayensu ne suke had su tun suna kanana kuma dole ne ya kasance tsakanin ‘yan uwan ​​juna.  Duk da haka, a bikin Gerewol na shekara, mazan Wodaabe suna sanya kayan ado da kayan kwalliya da kuma yin ka raye-raye don burge matan – kuma da fatan sace sabuwar mata.

 Idan namiji ya iya  sata mace musamman daga mijin da ba zai so ya rabu da matarsa ​​ba to Zasu zama sanannu a cikin al’umma.

  1. Tofa yawu a matsayin nau’in gaisuwa na kabilar Maasai

 Kabilar Maasai, da ake samu a Kenya da Tanzaniya, suna tofa yawun bakinsu a matsayin wata hanya ta gaisuwa.  Yayin da Bature zai ce sannu watto hello, toh su tofa yawu ne  hanyar gaisuwan su.

 Baya ga haka, idan aka haifi jariri, al’adar maza ne su  tofawa jariri yawun a ce masa mara mugu.  Sun yi imanin cewa wannan zai kare jariri daga mugayen abubuwa.  Mayakan Maasai suma suna tofa yawun  bakinsu a hannun su kafin  su yi gaisuwa da dattijai.  Bugu da ƙari, kabilar Maasai kuma ta shahara da shan jinin dabba.

  1. Bikin matattu – Malawi

Al’ummar Chewa ƙabilar Bantu ce da aka fi samun su a Malawi. A yayin bikin jana’izar dan kabilar, ya zama al’ada a wanke gawar Wadda ya mutu. Ana kai gawar zuwa wani wuri mai tsarki inda ake tsarkake gawar ta hanyar tsaga makogwaro da zuba ruwa ta cikin mamacin.

Ana matse ruwan daga jiki har sai ya fito da tsabta.  Daga nan sai a debo ruwan a yi amfani da shi wajen shirya abinci ga daukacin al’umma.

  1. tsalle kan bijimi a Habasha

 A Habasha, samarin matasa dole ne su yi wani nau’i na al’ada don tabbatar da kasancewarsu namiji wannan ya ƙunshi abubuwa da yawa.

 Yaro matashi dole ne ya tube tsirara, ya gudu, ya yi tsalle ya sauka a bayan bijimi.  Daga nan sai a bi ta bayan bijimai da dama da aka jera a cikin garke madaidaiciya da saƙa da wutsiya da ƙahoni da manyan mutane suka ja.  Ana kiran wannan al’ada da Hamar.

  1. Gwajin karfin namiji a Uganda

 A cikin kabilar Banyankole, ƙabilar tsiraru da ke zaune a Uganda, aure yana nufin nauyi sosai ga  yaruwan mahaifin amaryan watto aunty.

 Lokacin da ma’aurata suke so su yi aure, yaruwan mahaifin amaryan za ta yi jima’i da ango a matsayin “gwajin ƙarfinsa ” sannan kuma, dole ne ta gwada budurcin amarya.

  1. Shan Duka don samun mace na kabilar fulani

 Yan Kabilar Fulani na yin Sharo kafin su yi aure.  Anan ango na shan Duka daga hannun manyan  domin ya samu matar Aure da mutunci.  Idan namiji bai iya jure zafin dukan ba, sai a fasa daurin aure.

 Baya ga shan Duka, dangin amarya za su iya karbar Koowgal, wanda zabin biyan sadaki ne ko kuma Kabbal, bikin Musulunci mai kama da aure amma babu ango da amarya.

  1. Miƙewar leɓe na  Habasha da Sudan

 Ana samun mutanen kabilar Surma a kudancin Sudan da kuma kudu maso yammacin kasar Habasha.  A lokacin yanmatanci, ana yi wa mata mikewar leɓe wanda ya haɗa da cire ƙananan haƙora don ɗaukar farantin leɓe;   ana ƙara girman farantin leɓen a duk shekara har sai ya zama girma mai ban mamaki.

 Wasu daga cikin mazan suna yin irin wannan mikewar jiki da kunnuwansu.  Har ila yau, suna horar  mayakansu  ta hanyar yi musu tabo, sunyi imanin cewa  tabon da suke da shi, sun fi jan hankalin mata ‘yan kabilar.

By: Firdausi Musa Dantsoho