Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci a kai mata Sheikh Abduljabbar gabanta
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kano ta bayar da umarni ga hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa da ta gabatar da Sheikh Abduljabbar Kabara a gaban kotu domin ci gaba da sauraron ƙarar da ya ɗaukaka.
Sheikh Abduljabbar, malamin addinin Musulunci, na tsare a gidan yari ne bayan wani hukunci da Ƙaramar Kotun Shari’a ta yanke, inda ta same shi da laifin batanci tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A yayin zaman, jagoran alkalai, mai shari’a Mohammed Lawal Shuaibu, ya bayyana cewa tun da wanda ya shigar da ƙarar ya yi hakan da kansa ba tare da lauya ba, dole ne ya bayyana a gaban kotu domin kare kansa da hujjojinsa.
Haka kuma, kasancewar yana tsare, an umarci hukumar gidan yari da ta gabatar da shi a ranar 23 ga Afrilu, 2026 domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Afrilu domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Hafsat Ibrahim



