An fara aikin fadada hanyoyin gundumar Mpape tare da tsabtace su.

0
127

Bayan watanni takwas, , a ranar Laraba, an  kaddamar da aikin ci gaba da gudanar da aikin tsaftar muhalli domin ceto mutanen Mpape daga kangin ababen hawa da masu aikata laifuka.

Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tilastawa Ministan babban birnin tarayya, Ikharo Attah, ya ce bayan watanni takwas da suka gabata na ruguza  haramtattun gine-ginen sun sake kunno kai a kan titunan , wadanda suka zama mafakar masu anfani da miyagun kwayoyi a yankin.

Ya bayyana cewa hukumar ta samu korafe-korafe na ayyukan da suka saba wa doka daga yankin Crush rock har zuwa tsohuwar kasuwar da ke kan hanya.

Attah ya ce, tsaftace muhallin zai kara habaka tsaftar birnin, da yaki da ta’addanci da kuma dakile yadda ake samun rahotannin aikata laifuka.

Ya bayyana cewa dole ne a duba ayyukan haramtacciyar hanya a yankin Mpape da ke daura da gundumar Maitama a Abuja.

“Bayan watanni takwas mun dawo Mpape saboda masu laifin sun koma yankin, mun samu rahoton cewa sun dawo, don haka ya zama wajibi mu gaggauta zuwa mu wanke su.

“Muna yin abubuwa guda biyu a nan, sake duba aikin tsaftar muhalli, ‘yantar da hanya, kutse da kuma dakile ayyukan muggan laifuka musamman a yankin.

“Mun kuma kakkabe maboyar ‘yan ta’adda a bayan yankin bankunan da ke zama cibiyar kasuwanci, hakan ya nuna cewa muna samun nasara a yakin da muke da masu aikata laifuka a Mpape.”

 

Daga Fatima Abubakar.