Friday, September 22, 2023
Home DANDALIN NISHADI Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 66 a duniya.

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 66 a duniya.

0
59

A ranar Laraba ne da ya gabata,Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mairitaya),ya bi sahun daukacin al’ummar Musulmi wajen taya Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III murnar cika shekara 66 a ranar 24 ga Agusta, 2022.

Sakon shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yammacin ranar Laraba ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu.

Sanarwar mai taken ‘Shugaba Buhari ya taya Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III murnar cika shekaru 66 a duniya.’

Buhari ya bayyana sarkin a matsayin shugaban addini wanda ke son ci gaban al’umma da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a kasar nan ta hanyar ba da shawara akai-akai ga cibiyoyi da kwararru da ma’aikatan gwamnati don bin ka’idojin da aka amince da su.

“Shugaba Buhari ya yabawa Sarkin Musulmi bisa irin rawar da yake takawa na kishin kasa a kodayaushe na bayar da shawarar samar da ingantacciyar Najeriya ta hanyar yin aiki tare da shugabannin addini, gargajiya da na siyasa don jagorantar mabiya a koyaushe kan yin zabin da ya dace.Tare  da kiyayewa  da tabbatar da kyakkyawar makoma.

Sanarwar ta kara da cewa, “Yayin da mai girma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya ke cika shekaru 66, shugaban kasar ya amince da halin girma,jajircewa da kuma  sadaukarwar Sarkin Musulmi tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2006.”

Don haka Buhari ya yi addu’ar samun lafiya ga shugaban da iyalansa.

Daga Fatima Abubakar.