An Ga Sabon Wata Yayin Da Sarkin Musulmi Ya Sanar Da Ranar Sallar Eid-Al-Kabir

0
68

 

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa ranar Litinin 19 ga watan Yuni ce za ta kasance daya ga watan Zul-Hijja 1444AH.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Wali Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Sokoto.

“Kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi tare da kwamitin ganin wata na kasa a ranar Lahadi sun samu rahoton ganin jinjirin watan Dhul-Hijja 1444AH.

“Sarkin ya karbi rahoton kuma ya bayyana ranar Lahadi 19 ga watan Yuni a matsayin ranar farko ga Zul-Hijja 1442AH,” in ji wani bangare.

Zul-Hijja wata ne na 12 a cikin kalandar Musulunci, wanda a cikinsa ne musulmi suke gudanar da aikin Hajji tare da gudanar da bukukuwan layya.

Yanzu haka Musulman Najeriya za su gudanar da Sallar Idin Al-Kabir na shekarar 2023 a ranar Laraba 28 ga watan Yuni, daidai da 10 ga Zul-Hijja 1444AH.

Firdausi Musa Dantsoho