An nada Ibrahim Aminu daga jahar Katsina a matsayin sakataren ci gaban al’umma ta FCTA.

0
30

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi sabon sakatariyar cigaban al’umma ta FCTA, Ibrahim Aminu da ya yi watsi da ayyukan raba kan jama’a wajen gudanar da ayyukan sa, tare da la’akari da cewa Abuja babban birnin tarayya ne ba Katsina ba ce in da ya fito.

Wike ya ce dole ne wadanda aka nada a FCT su yi wa kowa hidima ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, domin Nijeriya ta kowa ce.

Ministan ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar dawo da fata ga ‘yan Najeriya ta hanyar aiwatar da manufofin da suka dace da mutane.

A cewarsa, wadanda aka nada a FCT dole ne su yi aiki don tallafawa “sabuwar bege na shugaban kasa” sannan kuma su kasance a shirye don yin lissafin ayyukansu.

Wike ya ce, “’Yan Najeriya  suna cikin yanayi, don haka akwai bukatar sabunta ajandar fatan Mista Shugaban kasar.

“Ba ’yan Katsina kadai za ku yi wa hidima ba don kowa dan Najeriya ne.

“Ku tuna cewa a karshe za a tuhume ku. ‘Yan Najeriya sun gaji da samun uzuri a koda yaushe”

 

Daga Fatima Abubakar.