Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar bayar da sammacin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da wasu daraktocin bankunan kan kin amsa gayyatar da kungiyar Green Chamber ta yi masa akan karancin sabbin takardun kudi na naira uku.
Majalisar dai ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN da daraktocin bankin ne a akan dakatar da ansan tsofofin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1,000 daga ranar 31 ga watan Junairu 2023 amma shugabannin bankin sun ki amsa gayyatar da Green Chamber suka yi masa.
Gbajabiamila, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce shugabannin bankunan, ta hanyar yin watsi da gayyatar majalisar, sun ci mutuncin hukuma da hurumin majalisar. “Wannan ba abin da za,a yarda da shi ba ne,” in ji shi.
Ko da yake shugaban majalisar a cikin sanarwar da ya bayar a ranar Alhamis, ya ce takardar sammacin da za a bayar za ta shafi babban bankin CBN da daraktocin bankuna ne amma bai fito fili ya ambaci Emefiele ba, majalisar a lokuta daban-daban cikin watanni biyun da suka gabata ta gayyaci gwamnan babban bankin na CBN kan sake fasalin naira. amma bai ansa gayyatar ba.
Majalisar dai ta gayyaci Emefiele da daraktocin bankin ne domin su bada dalilan da suka kasa fitar da sabbin kudaden da aka yi fasali kafin ranar 31 ga watan Junairu, 2023.
Majalisar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Ado Doguwa kan lamarin.
Shugaban majalisar ya ce, “Kudirin da majalisar ta yanke ya kasance ne kan bayanan da ke nuna cewa fitar da takardar kudin Naira da aka sake fasalin ya yi kasa a gwiwa. Wannan gazawar tana da sakamako na gaske kuma mai muni kan ikon ‘yan Najeriya na gudanar da kasuwanci a fadin kasar.
“Kin amincewar da CBN ya yi na amsa gayyatar da ‘yan majalisar wakilai suka yi masa ya nuna rashin mutunta rayuwar al’ummar Najeriya wadanda abokan cinikinsu ne. Haka nan cin fuska ne ga hukuma da hurumin majalisar jama’a.
“Saboda haka, bisa ga ikon da sashe na 89 (1) (d) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya ya bayar da kuma oda na 19 (2) (1) na Dokokin Majalisar Wakilai, ba zan yi kasa a gwiwa ba. a bayar da sammaci ga Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da ya tilasta wa babban bankin CBN ko Manajan Daraktocin da suka gaza, ko suka ki amsa sammacin da Majalisar Wakilai ta yi.”
Ya kara da cewa majalisar ta amince da ikon CBN na tantance kudaden da kasar ke bukata da kuma dawo da kudaden tare da sanarwa mai ma’ana, bisa amincewar shugaban kasa.
“Majalissar tana kuma sane da cewa dokar babban bankin Najeriya sashe na 20 (3) ta umurci CBN da ta fanshi darajar kudin da aka dawo da ita idan ana bukata, koda bayan karewar sanarwar dawo da kudin.
“Duk da wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanya, majalisar za ta tabbatar da cewa an mutunta wannan tanadin dokar.”
A ranar 26 ga Oktoba, 2022 ne CBN ya bayyana shirinsa na sake fasalin takardun kudi guda uku. Daga nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, yayin da babban bankin ya sanya ranar 31 ga watan Janairu domin dakatar da amfani da tsoffin takardun.
Bankin na CBN ya kuma kayyade iyakokin fitar da kudade na mako-mako zuwa N500,000 ga daidaikun mutane da kuma N5m na kamfanoni.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho