An gano gawar tsohon dan wasan Ghana Christian Atsu bayan wata girgizar kasa da ta afku a kasar Turkiyya, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayana.
Atsu, mai shekaru 31, ya mutu a girgizar kasa mai karfin awo 7.8 da ta afku a Turkiyya da Siriya a ranar 6 ga watan Fabrairu, inda ta kashe mutane fiye da 43,000 a kasashen biyu.
Akwai rahotannin farko da aka kubutar da shi kwana guda bayan girgizar kasar, amma sai suka zama karya.
Manajansa a Turkiyya Murat Uzunmehmet ya shaidawa menema labaran da cewa an gano gawarsa a karkashin kasa a lardin Hatay da ke kudancin Turkiyya.
“Mun kai gawarsa babu rai. Ana ci gaba da kwashe kayansa. An kuma samu wayarsa,” Uzunmehmet ya ce.
Tsohon kulob dinsa na Newcastle United ya tabbatar da rasuwarsa da sanyin safiyar Asabar.
Kungiyar ta rubuta “Mun yi matukar bakin ciki da jin labarin cewa tsohon dan wasanmu Christian Atsu ya rasa ransa cikin bala’i a girgizar kasar Turkiyya.”
“Mai hazaka kuma mutum na musamman, ‘yan wasanmu, ma’aikatanmu, da magoya bayanmu za su rika tunawa da shi a koyaushe.
Dan Ghana wadda ake alfahari ya bugawa kasarsa wasa sau 65, Christian ya wakilci kungiyarmu tsakanin 2016 da 2021, inda ya buga wasanni 121.”
Dan wasan tsakiya Atsu ya shafe shekaru hudu a Chelsea kafin ya koma Newcastle na dindindin a 2017. Ya sanya hannu a watan Satumba a kungiyar Hatayspor ta Turkiyya Super Lig.
Ma’aikatan bincike da ceto sun gano gawar Atsu a inda yake zaune a gidan Ronesans, wani katanga na wasu manyan gidajen alfarma da suka ruguje a birnin Antakya na Hatay.
‘Yan sandan Turkiyya sun kama dan kwangilar ginin a filin jirgin saman Istanbul a makon da ya gabata a daidai lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Montenegro.
Daga Safrat Gani