Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce jam’iyyar APC ba za ta sha wuya ba wajen lashe zaben 2023 ba.
Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba bayan ya kaddamar da wani hostel mai sunan shi a jami’ar Al-Hikmah da ke jihar Kwara, Masari ya ce masu cewa zai yi wuya jam’iyya mai mulki ta yi nasara “ba su san abin da suke fada ba sam”.
Gwamnan ya ce al’amuran da suka shafi Najeriya “matsala ce ta duniya” kuma wasu kasashe suna fama da irin wannan matsala. “Wadanda ke cewa zai yi wahala APC ta ci zabe mai zuwa, sam ba su san abin da suke fada ba,” inji shi.“Abin da suka ce a 2019 ke nan cewa zai yi wuya jam’iyyar APC ta samu nasara, saboda halin da kasar ke ciki, amma sai ga shi sun yi kuskure. “Abu mai mahimmanci shine batun da ya shafi wannan ƙasa yana da girma a duniya. Duk duniya na fuskantar rikici da hauhawar farashin kayayyaki. “Amurka na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi muni a cikin shekaru 40 da suka gabata, haka ma Ghana, Nijar, da kuma kasashen makwabta. Dole ne mu fahimci abin da ke faruwa a duniya kafin mu yi suka ba tare da la’akari da batun da ke duniya ba. Matsalolin da muke da su sun wuce abin da kasa daya za ta iya magancewa.” Masari ya ce kowane dan kasa yana da rawar da zai taka wajen taimakawa hukumomi wajen magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta. “Ina daukar wannan a matsayin wani lokaci mai wucewa a cikin tafiyar ci gabanmu,” in ji shi.
UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.